Babu hukunci kan wadanda suka kashe Turawa — Mugabe

Robert Mugabe Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Robert Mugabe ya sha cewa an yi kuskure wajen shirin tsarin mallakar filaye na kasar

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, ya ce bai kamata a gurfanar da wadanda suka kashe a manoma fararen fata a lokacin da aka yi shirin sauya fasali na tsarin mallakar filaye na kasar.

Mista Mugabe ya sanar da 'yan kasar hakan ne a wajen wani taro na bikin girmama gwarazan kasar, a Harare, babban birnin Zimbabwe.

Ya ce, "Kwarai akwai wadanda aka kashe saboda sun hau kujerar na ki. Ba za mu taba gurfanar da wadanda suka kashe su ba. Na tambaya, don me za mu kashe su

Masu amfani da shafukan sa da zumunta dai sun yi ta mayar da martani kan kalaman Shugaba Mugabe.

A lokacin mulkin mallaka dai, an ware gonakin da suka fi kyau da daraja ne ga Turawan da ke kasar, a shekarar 2000 kuma, Mista Mugabe ya jagoranci kwace gonakin daga wasu Turawa kusan 4,000.

Mista Mugabe dai ya sha nanata cewa an yi ba daidai ba a shirin tsarin mallakar filaye mai cike da ce-ce-ku-ce na kasar.

A shekarar 2015 ya ce, "Ina tsammanin gonakin da muka bai wa mutane suna da matukar girma. Ba za su iya kula da su ba."

Ana ganin kwace gonakin da aka yi daga hannun Turawa shi ne sanadin tabarbarewwar arzikin Zimbabwe tun shekara ta 2000.