Saliyo: Za a yi wa daruruwan gawawwaki jana'izar gama-gari

Mutuwaren Freetown

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Har yanzu dai ba a san inda mutane 600 suke ba.

Yau Alhamis ne gwamnatin kasar Saliyo ta ce za a yi wa wadanda aka tabbatar sun mutu sakamakon ambaliya da zaftarewar kasa a wajen babban birnin kasar, jana'izar gama-gari.

Amma wasu jami'an kiwon lafiya a Saliyon sun ce an binne kusan rabin mutane 400 da kawo yanzu aka san sun mutu sakamakon ibtila'in na ranar Litinin a birnin na Freetown, gabanin jana'izar ta hukuma saboda sun fara rubewa.

''Tun jiya sun gano fiye da gawawwaki 400 kuma an binne kusan 150 cikin dare, wadanda suka rube kwarai na manya da yara. A halin yanzu muna jiran izni ne mu fara jana'izar ta gama-gari domin akwai wasu gawwakin a cikin mutuware da ke bukatar a binne su cikin gaggawa domin sun rube.'' Inji Alisine Sesa ma'aikaciyar lafiya mai aikin sa-kai a birnin na Freetown.

Shi ma Dr. Simeon Owizz Koroma babban mai binciken gawa na birnin Freetown ya shaida wa BBC cewa ba mamaki a ci gaba da samun gawawwakin wadanda wannnan ibtila'i ya afkawa har nan da wata daya ko biyu masu zuwa:

''Gawawwakin da muka tantace sun kusan kai 350 amma muna tsammanin a kawo wasu kari daga nan har zuwa wata daya ko biyu don na san akwai wadanda gine-ginen gidaje suka rufe.''

Hukumomin dai sun ce sun daga jana'izar ne zuwa ranar Alhamis domin bai wa damar gane gawawwakin 'yan uwasu da suka mutu.