Saliyo: An umarci masu makwabtaka da tsauni da su kaura

Unguwar Regent da ke Freetown

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Jami'ai sun ce gwamnati na daukar matakan gina gidaje masu saukin kudi don sake tsugunar da su.

Mahukunta a Saliyo sun umarci mazauna yankin Regent, unguwar da masifar zabtarewar kasar ta halaka daruruwan jama`a da su kaura zuwa wani wuri saboda yankin na fuskantar yiwuwar sake zabtarewar kasa a nan gaba.

An dai yi jana`izar akalla mutum 550, wandanda masifar zabtarewar kasa da ambaliya suka halaka, yayin da alkaluma ke cewa har yanzu ba a ji duriyar wasu mutum 600 ba.

Hukumar kula da al`amuran da suka shafi bala`i a kasar ta ce tun aukuwar masifar ta dukufa wajen gano musabbabin hadarin da hanyoyin kare aukuwarsa gaba; kuma ta gano ya zama dole mutanen gangaren su kaura.

''An gudanar da bincike a kan darewar da wannan tsauni ya yi, kuma an fahimci cewa akwai kimanin tsawon kilomita tara na bangaren wannan kasa da wannan darewar ta shafa, kuma yana fuskantar barazanar zabtarewa a nan gaba. Don haka ba za mu zuba idon mu tabka wata asarar al`umma mai wannan yawa ba.'' Inji Mista Nabi Kamara, wani jami`i a hukumar.

Ya kara da cewa gwamnati na daukar matakai da nufin gina gidaje masu saukin kudi don sake tsugunar da su.

Sai dai da dama daga cikin mazauna yankin irinsu Mista Lansana Kamara - wani dattijo da ke makwabtaka da gidajen da kasa ta binne a unguwar, sun ki tashi daga gidajen nasu suna cewa ba su da inda za su koma.

''Na shafe shekara 39 ina soja, kuma da dan kudin da gwamnati ta sallame ni ne na gina wannan gida, wanda nake zaune da matana biyu da `ya`ya goma sha daya. Idan gwamnati ta ce mu tashi daga nan ina zan kai wannan gayyar da ke gidana? Idan na gusa daga nan ba ni da wani katabus, saboda tsufa ya kama ni!''

A halin da ake ciki dai jami`an gwamnati da na kungiyoyin agaji sun dukufa suna ta lallashin mutanen da nufin shawo kan magidantan da suka ki tashi ko za su amince su kaura.

Abin da ba a sani ba shi ne, ko za a kai wata gabar da gwamnati za ta sa karfi, idan lalama ba ta ci ba.