Ambaliya: Mutane miliyan 16 sun shiga mawuyacin hali a Asiya

Wani yanki a kasar Indiya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kimanin mutane miliyan 11 ne ambaliya ta shafa a Indiya

Jami'an agaji na kasa-da-kasa sun ce fiye da mutane miliyan 16 ne ambaliyar ruwan da ake yi duk shekara a kudancin Asiya ta shafa.

Ana tsammanin ambaliyar ruwan ta hallaka kusan mutane 500 kawo yanzu a kasashen Nepal, da Bangaladesh da kuma Indiya; kuma ana jin lamarin zai dada muni.

Gamayyar kungiyoyin agaji na kasa da kasa IFRC ta ce ambaliyar ta kusan zaman bala'i mafi muni a yankin cikin shekaru.

Jami'ai a Bangaladesh dai sun ce ambaliyar ta mamaye kusan kashi da ya bisa uku na fadin kasar sakamakon cikowar da ba a saba ganin irinta ba daga wasu koguna da ke Indiya.

Arewacin kasar ne dai ya fi tagayyara inda ruwan ya kakkatse hanyoyin isa wasu yankunan.

''Haka kuma ruwan sun hadiye gidaje da makarantu da wasu gine-ginen kuma yayin da da ruwan ke ci gaba da kwararowa daga kogunan kasar Indiya wadanda suka cika suka batse; akwai fargabar lamarin ya kara muni'' inji wani wakilin BBC a birnin Dhaka.

Ma'aikatan agaji da kuma jami'an hukumomin bayar da agajin na gwamnati aiki tukuru domin kai agajin abinci da sauran abubuwa ga wadanda lamari ya shafa.

Akwai dai dogayen layukkan mutane da ke jiran samun tallafin inda wasunsu ke kokawa cewa agajin da suke samu baya isarsu.

Amma wani babban jami'in bayar da agajin gaggawa na gwamnati ya shaidawa BBC cewa suna kan shawo kan matsalar kuma suna da tabbacin abubuwa za su gyaru.