Shugaba Buhari na kan hanyar komawa gida yau Asabar

Shugaba Muhammadu Buhari
Image caption Buhari dai ya shafe fiye da kwana wata uku a Landan

Fadar Shugaban Najeriya ta ce nan gaba a yau Asabar ne ake sa ran Shugaba Muhammadu Buhari zai koma gida bayan wata doguwar jinya a birnin Landan.

A cikin wata sanarwa da Mai bai wa shugaban Shawara kan watsa labarai Femi Adesina ya fitar ya ce ana sa ran shugaban ya yi wa 'yan kasar jawabi ta gidajen rediyo da talbijin ranar Litinin da safe.

''Ya gode wa daukacin 'yan Najeriya wadanda suka yi ta yi masa addu'ar samun lafiya da fatan alheri tun lokacin da ya fara jinya,'' inji takaitacciyar sanarwar mai sakin layi hudu.

Shugaba Buhari dai ya bar kasar ne ranar 7 ga watan Mayu domin jinyar rashin lafiyar da ba a bayyana ba; bayan ya mika ragwamar shugabancin kasar ga mataimakinsa wanda ya kasance mukaddashin shugaban kasar tun sannan.

Wannan dai shi ne lokaci mafi tsawo da wani shugaban kasar ya taba kwashewa yana jinya a kasar waje kuma dawowar tasa na zuwa ne 'yan kwanakki bayan da wasu 'yan kasar suka fara zanga-zanga suna kiran ya dawo ko ya yi murabus.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Ku kalli bidiyon gidan da Buhari yake jinya a London

Rashin lafiyar Buhari tun farkon shekarar 2017

 • 19 ga watan Jan - Ya tafi Birtaniya domin "hutun jinya"
 • 5 ga watan Fabrairu - ya nemi majalisar dokoki ta kara masa tsawon hutun jinya
 • 10 ga watan Maris - Ya koma gida, amman bai fara aiki nan-da-nan ba
 • 26 ga watan Afrilu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba kuma "yana aiki daga gida"
 • 28 ga watan Afrilu - Bai halarci Sallar Juma'a ba
 • 3 ga watan Mayu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba a karo na uku
 • 5 ga watan Mayu - Ya halarci sallar Juma'a a karon farko cikin mako biyu
 • 7 ga watan Mayu - Ya koma Birtaniya domin jinya
 • 25 ga watan Yuni - Ya aikowa 'yan Najeriya sakon murya
 • 11 ga watan Yuli - Osinbajo ya gana da shi a London
 • 23 ga watan Yuli - Ya gana da wasu gwamnonin APC da shugaban jam'iyyar
 • 26 ga watan Yuli - Ya sake ganawa da wasu gwamnoni ciki har da na PDP
 • 4 ga watan Agusta- Ya gana da Archbishop na Canterbury, Justin Welby
 • 13 ga watan Agusta - Ya gana da wasu daga cikin jami'an gwamnatinsa
 • 18 ga watan Agusta - Ya gana da Fasto Enoch Adeboye

Labarai masu alaka