Shin ko har yanzu ana amfani da biro wajen rubutu?

Yanzu kasuwar biro ta ja baya saboda shigowar abubuwan rubutu na zamani Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Biro

Tun bayan bullar sabbin hanyoyin rubutu kamar Komfuta da wayoyin salula, kasuwar alkalami ko kuma biro ta ja baya.

A Najeriya ma dai haka abin ya ke, domin da yawa daga cikin al'ummar kasar musamman matasa da manya ma'aikata, su kan jima ba su yi rubutu da biro ba, saboda sun fi amfani da wayoyinsu na salula ko kuma idan a wajen aiki ne da Komfuta.

A halin da ake ciki a yanzu, ko da sako ne mutum zai rubuta, to da sabbin hanyoyin rubutun na zamani ake amfani.

Yawanci dai a yanzu dalibai 'yan makarantun Firamare da na gaba da ita wato Sakandire ne ke amfani da biro wajen rubutu.

Masu sayar da irin abubuwan rubutu wadanda ba na zamani ba sun ce gaskia tun bayan bullar abubuwan rubutun na zamanin, kasuwarsu ta ja baya ba kamar da ba.

To amma sun ce, duk da bullar abubuwan zamanin na rubutu, dole a cigaba da amfani da biro, dan akwai abubuwa kamar zana jarrabawa.

A baya dai ba rubutu kadai ake yi da biro ba, har ma da ado, domin kuwa akan sanya shi a gaban aljihun riga musamman ga maza.

To amma yanzu al'amura sun canja, dan sau da dama zaka hadu da manyan mutane rubutu zai ta so sai kaji suna cewa ko akwai mai biro?