Matasan arewa sun yi abin da ya dace — ACF

Matasan arewacin Najeriya sun janye wa'adin ga 'yan kabilar Igbo Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Matasan arewacin Najeriya sun janye wa'adin ga 'yan kabilar Igbo

Kungiyar tuntuba ta dattawan arewacin Najeriyar, ta ce tun da matasan suka bayar da wa'adi na cewa al'ummar Igbo su tattara na su ya na su su koma yankunansu kafin 1 ga watan Oktoba mai zuwa, su ke ta tattaunawa da su domin samun maslaha.

A wata sanarwa da kungiyar ta raba wa manema labarai a Kaduna, ACF, ta ce matasan sun nuna da'a, da girmamawa ga shugabanninsu da kuma nuna son zaman lafiya a Najeriya baki daya.

Kazalika ACF, ta ce janye wa'adin da matasan suka yi zai rage zaman dar-dar din da aka shiga.

ACF, ta kuma yi kira ga shugabannin kabilar Igbo da su ma su kira matasansu su nuna musu illar wannan fitina da ta ta so.

Duk da janyewar wa'adin da gamayyar kungiyoyin matasan Najeriyar ta yi, ta bayar da wasu sharuda ga gwamnatin tarayyar da kuma gwamnatocin jihohin arewacin kasar.

Sharudan dai sun hada da cewa gwamnatin tarayya ta tanadi dokar da za ta bada dama ga dukkan mai son ballewa ko ficewa ya fice, da kuma gurfanar da Kanu gaban kuliya, sannan kuma kamfanonin da ke aiki a arewacin Najeriya, dole su tanadi guraben aiki da kaso 40 cikin 100 ga matasan yankin.