Wasu maniyyata a Najeriya sun fara fitar da rai da sauke faralli

Wasu maniyyatan bana a Najeriya sun fara kokonton zuwan su kasa mai tsarki domin sauke faralli Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A ranar Lahadi ne za a rufe filin jiragen sama ga mahajjatan bana a Saudi Arabia

Yayinda a gobe Lahadi ne ake sa ran hukumomin Saudi Arabia za su rufe filin jiragen sama na Jiddah ga jiragen mahajjatan bana, wasu maniyyata a Najeriya sun fara fitar da rai da zuwa kasa mai tsarki.

Maniyyatan da zuwa yammacin ranar Juma'a ba su samu tashi ba cikinsu ya duri ruwa domin suna ganin kamar za a hau arfar bana ba bu su.

Maniyyatan Jihar Neja ta arewacin Najeriya na cikin wadanda har yanzu ba su da tabbas a kan ko za su samu tashi.

Maniyyatan sun ce ana musu yawo da hankali, domin sai a kira su a kan cewa za su tashi, idan suka zo kuma sai a ce ba haka ba.

Kazalika sun kokawa da cewa har sun fara taba guzurinsu.

To sai dai kuma hukumar jin dadin alhazan jihar ta Neja ta musanta wannan zargin, inda ta ce ta na sa ne da halin da suke ciki kuma za a share masu hawaye.

Labarai masu alaka