Tamowa ta fara kama 'yan gudun hijirar Najeriya— ICRC

Mata da kananan yara ne suka fi shan wahala a cikin 'yan gudun hijira Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Miliyoyin 'yan gudun hijira na fama da kuncin rayuwa

Kungiyar bayar da agaji ta International Committee of the Red Cross ta ce har yanzu 'yan gudun hijirar da kungiyar Boko Haram ta fatattaka daga gidajensu a yankin tafkin Chadi na cikin mawuyacin hali.

Kungiyar ta ce ziyarar da ta kai wasu yankuna da bala'in hare-haren Boko Haram ya shafa, ta nuna mata cewa akwai sauran rina akaba game da tallafin da ake bai wa 'yan gudun hijirar, tana mai cewa babu abin da miliyoyon 'yan gudun hijirar ke so kamar samun zaman lafiya da komawa gidajensu.

Babban jami'in da ke kula da ayyukan bayar da agaji a yankin tafkin Chadi, Mamadou Sow, wanda ya kwashe kwana goma a arewa maso gabashin Najeriya ya shaida wa BBC cewa halin da ya tarar da 'yan gudun hijirar na da matukar muni idan akayi la'akari da cewa mutum miliyan biyar daga jihohin Adamawa da Borno da Yobe na matukar bukatar abinci.

Ya ce miliyan biyu daga cikinsu sun bar gidajensu ba su da damar komawa, ba su kuma da damar yin noma da kiwo da kuma kamun kifi.

Mamadou Sow, ya ce babu wanda wannan matsala ta fi shafa a yankin arewa maso gabashin Najeriya da ma yankin tafkin Chadi kamar mata da kananan yara, domin "za ka ga mace mai shayarwa ko mai ciki amma tana fama da tamowa, haka yara ma".

Saboda haka ya kamata a kara a kan taimakon da ake ba su musamman a irin yanayin da ake ciki na damuna.

Jami'in ya ce, duk 'yan gudun hijirar na samun taimako daga kungiyoyi da dama, dole gwamnatin Najeriya ma ta rubanya abin da ake ba su, bisa la'akari da cewa su ma ba a san ransu suka kasance a wannan yanayi ba.

Labarai masu alaka