Koriya ta Arewa za ta sake harba makami mai linzami

Kim Jong-un
Image caption Shugaban Koriya ta Kudu Kim Jong-un, ya na duba duba abin da suka kira makamin nukiliya da aka hada da sinadarin hydrogen

Koriya ta Kudu ta sanar da cewa ta ga alamun da suka nuna cewa Koriya ta Arewa na shirin sake gwajin wani makami mai linzami.

Hakan dai ya biyo bayan gwajin makami mai linzami da ke cin dogon zango da Koriya ta Arewar ta yi cikin kankanin lokaci.

Koriya ta Kudu ta gudanar da atisayen yadda za ta harba nata makamin.

Amurka ta yi gargadin cewa duk wata barazana da Arewa take yi a gare ta ko kawayenta lallai za a mayar mata martani da karfin soji.

A nata bangaren, Koriya ta Arewa ta ce nan ba da dadewa ba, za ta gwada wani makamin da aka hada shi da sinadrin Hydrogen, wanda zai ci dogon zangon da ka iya fadawa tsakiyar Amurka tun da karamin da aka harba a makwannin da suka wuce ya fada yankin Guam da ke tekun Pacific.

Haka kuma Arewar, ta ki nuna damuwa kan takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ke kara kakaba ma ta, inda ta ci gaba da kara kaimi kan makaman nukiliyarta.

Cikin watanni biyu da suka gabata, Koriya ta Arewa ta harba makamai masu linzami, inda ta harba wani da ya fada tekun Japan, wanda shugaba Shinzo Abe na Japan din ya ce ba za su yadda da duk tsokanar fadan da Arewa ke yi wa kasashen da ke yankinsu.

A ranar Litinin ne ake sa ran kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai yi taron gaggawa domin samo hanyoyin da za a magance matsalar ta da ta ki ci taki cinyewa.

Sai dai gabannin fara taron, shugabannin kasashen Koriya ta Arewa da Japan sun amince da matakin da Majalisar Dinkin Duniya za ta dauka na sake kakabawa Arewa takunkumi.

A watan Agusta Majalisar Dinkin Duniyar ta sanya wa Arewa takunkumin kan kayan da take fitarwa kasashen waje.

Labarai masu alaka