Nigeria: 'Ba mu ga kayan agaji a kasa ba'

Wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Benue sun ce suna cikin mawuyacin hali

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ambaliyar ruwan ta haddasa asarar dukiya da kadarori

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA, ta ce tuni ta fara kai kayan agaji ga mutanen da annobar ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Benue a makon da ya gabata.

Mai magana da yawun hukumar, Sani Datti, ya shaida wa BBC cewa, tuni aka fara rabon kayan da suka isa ga mutanen da ambaliyar ta shafa, musamman ga wadanda ke zaune a sansanonin da aka samar , wato wadanda ba za su iya komawa gidajensu ba.

Kakakin hukumar ya ce, ana raba wa mutanen kaya da suka hada da abin shimfida da abinci da makamantansu.

To sai dai kuma, duk da hukumar agajin gaggawan ta ce ana rabon kayan agajin, wasu da abin ya shafa sun ce ba su gani a kasa ba.

Don haka, suke kara kira ga gwamnatin tarayya da ta jihar da su tabbatar da cewa kayan agajin da aka tura domin a raba musu, an ba su dan suna cikin mawuyacin hali.

Mazauna wuraren da ambaliyar ruwan ta shafa sun ce sun rasa muhallansu da kadarorinsu, dan haka suke so a duba yanayin da suke ciki.

Ambaliyar ruwan da ta afku a wasu kananan hukumomi 12 a jihar ta Benue a makon da ya gabata , ta yi sanadiyyar raba mutane akalla dubu 100 da muhallansu.

Ko a ranar Lahadin da ta wuce ma anyi wani ruwan sama kamar da bakin kwarya a wasu yankuna na Jihar ta Benue, har ma kuma a ka samu asarar dukiyoyi, amma dai a wannan karon, ruwan saman bai yi barna sosai ba.

A cikin watan Yuli ne mahukunta a kasar suka yi gargadin cewa kusan jihohi 30 ne za su fuskanci bala`in ambaliyar ruwa a bana, sakamakon mamakon ruwan sama da ake tafkawa.