Nigeria: Yadda ruwa ya tafi da dalibai biyar a Kaduna

kwale-kwale Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ko a kwanan nan ma sai da haduran kwale-kwale ya kashe mutane a jihohin Kebbi da Neja da Legas

Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya ta tabbatar da cewar kogin Kaduna ya ci 'yan makarantar sakandare biyar masu ziyarar karo ilimi.

Rundunar ta bayyana cewa daliban da suka fito daga makarantar Victory International School, sun hau kwale-kwale daga wata tashar zuko ruwa ta hukumar samar da ruwan sha mallakar jihar kusa da tashar jirgin kasa da ke a lokacin da lamarin ya faru da su.

Bayan daliban su goma sun kammala ziyarar karo ilimin a tashar hukumar samar da ruwan ne sai suka hau kwale-kwale domin haye kogin.

Sai dai kwale-kwalen da suka hau din ya dare biyu domin yawan mutanen da ke kai, lamarin da ya sa daliban suka nutse.

Masu aikin ceto sun samu damar ceto biyar daga cikin daliban. An kuma samu gawarwakin biyu daga cikinsu yayin da har yanzu ake neman sauran gawarwakin.

Lamarin dai ya auku ne a ranar Laraba.

Labarai masu alaka