Titanic: An sayar da wasiƙa naira miliyan 60

Titanic letter Hakkin mallakar hoto HENRY ALDRIDGE & SON
Image caption Oscar Holverson ne ya rubuta wasikar zuwa ga mahaifiyarsa shekara 105 da ta wuce

An sayar da ɗaya daga cikin wasiƙun da suka rage kuma aka san an rubuta su a cikin jirgin ruwa na Titanic a kan kuɗi mafi tsada a duniya, yayin wani gwanjo.

Wasiƙar wadda wani ɗan kasuwa Ba'amurke kuma fasinjan jirgin Titanic da hatsarinsa ya yi suna a duniya, Oscar Holverson, ta janyo kuɗi fam na gugar fam har dubu 126 kwatankwacin naira miliyan 60.

An yi rububin wannan wasiƙa saboda Oscar ya rubuta ta ne sama da shekara 100 lokacin da suke tafiya a cikin jirgin.

Jirgin Titanic ƙirar Belfast ya ci karo da wata gundumemiyar ƙanƙara a tsakiyar teku ranar 14 ga watan Afrilun 1912, kwana guda bayan rubuta wasiƙar.

Ita ce wasiƙa guda da ta rage kuma aka san an rubuta ta a cikin jirgin, har ta tsira daga iftila'in na Tekun Atlanta.

An sayar da takardar wadda duk ta yi jirwaye ga wani mutumin Burtaniya, wanda ya yi tayinsa ta hanyar wayar tarho a gwanjon da aka buga mata cikin yankin Wiltshire.

Mai buga gwanjon, Andrew Aldridge, ya bayyana mutumin da ya yi sa'ar sayen wasiƙar wanda ba a bayyana sunansa ba, da cewa "ya dace da samun muhimman kaya na tarihi".

Hakkin mallakar hoto HENRY ALDRIDGE & SON
Image caption Mista Oscar dan kasuwa ne mai tashe a Amurka

Ɗan kasuwar mai tashe, Mista Oscar Holverson ya rubuta wasiƙar zuwa ga mahaifiyarsa ne a lokacin da suke tafiya cikin wannan jirgi da ƙaddara ta faɗa masa tare da matarsa, Mary.

Ma'auratan sun shiga jirgin ne a Southampton da zimmar komawa gidansu a birnin New York.

A cikin wasiƙar, marubucin ga alama na cike da kakabi na abin da ke zagaye da shi, inda yake faɗa wa mahaifiyarsa cewa "jirgin katafare ne kuma yana da kayan alatu tamkar wani ƙanƙareren otel".

Mista Holverson, wanda ke da salo na daban irin nasa wajen shirya li'irabi (tsarin rubuta jimloli), ya kuma yi bayani a kan ganin "mutumin da ya fi kowa kuɗi wancan lokaci a duniya" - John Jacob Astor - a cikin jirgin, cikin rakiyarsa mai ɗakinsa.

"Idan kika gan shi kamar sauran mutane, duk da yake ya tara miliyoyin kuɗi," in ji shi. "Sun zauna a farfajiyar jirgin kamar kowannenmu."

An yi wa wasiƙar farashin kuɗi tsakanin fam dubu 60 zuwa dubu 80.

Da yake jawabi gabanin sallama wasiƙar ranar Asabar, Mista Aldridge ya ce "ko wasiƙar ta goge kwata-kwata, za a sanya ta cikin kayan tarihin da aka fi rububi, saboda darajar tarihi da zubinta".

A matsayinsa na mutumin da ya yi gwanjon kayan tunawa da jirgin Titanic tsawon shekara 20, ya ce ƙunshin wasiƙar ya kai ta ga wani matsayi, "saboda daɗewarta, da kuma sanin cewa ta je tsakiyar Tekun Atlanta kuma ta alkinta abin da take ƙunshe da shi".

Ɗaya daga cikin fatan da Oscar Holverson ya yi a cikin wasiƙar bai taɓa tabbata ba, inda ya rubuta cewa: "Idan komai ya tafi daidai za mu isa New York ranar Laraba da safe."

Lokacin da jirgin Titanic ya nutse, Oscar shi da mutumin da ya fi kowa kuɗi, JJ Astor, sun mutu tare da mutane fiye da 1,500.

Matarsa dai, Mary Holverson ta tsira.

An gano gawar mijinta, inda aka tsinci wannan wasiƙa cikin wani ɗan littafi da ake zura shi aljihu.

Hakkin mallakar hoto HENRY ALDRIDGE & SON
Image caption Wasikar ta shiga hannun mahaifiyar Oscar duk da yake ba ta dauke da hatimi

Har yanzu tana ɗauke da dabbare-dabbaren ruwan teku da kuma tambarin tsaro na kamfanin sufurin jiragen ruwa na White Star Line.

Daga bisani dai wasiƙar ta je hannun wadda aka rubuta dominta.

An binne Mista Oscar Holverson ne a maƙabartar Woodlawn da ke New York, ba tare da sanin cewa nan gaba bayan shekara 105, wasiƙarsa za ta samu irin wannan ɗaukaka ba.

Mai gwanjon Mista Aldridge, wanda kuma shi ne ya sayar da komai kama daga wasu mukullan jirgin Titanic a kan fam dubu 85, zuwa wata garaya da aka kaɗa a lokacin da jirgin ke nutsewa a kan kuɗi fam miliyan 1 da dubu 100, ya ce ya yi farin ciki da ya yi tsawon ran ganin wannan wasiƙa.

Ya ce tana "ɗaya daga cikin muhimman kayayyaki mafi daraja daga jirgin Titanic da aka yi gwanjonsu kuma hakan ya nuna irin gagarumar sha'awar da jirgin da ma fasinjojinsa ke da ita a zukata.

Wasiƙar da aka sayar yayin wani gwanjo a baya cikin watan Afrilun 2014, ta yi darajar kudi har fam dubu 119, ita dai an rubuta ta ne sa'o'i ƙalilan kafin jirgin ya ci karo da ƙanƙara.

Labarai masu alaka