Bahagon Kanawa da Mai Kifi sun yi canjaras
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Bahagon Kanawa da Mai Kifi sun yi canjaras

Dambe tara aka yi a gidan wasa na Ali Zuma da ke unguwar Dei-Dei a Abuja Nigeria a safiyar Lahadi.

Cikin wasan har da wanda aka yi turmi biyu babu kisa tsakanin Bahagon Kanawa daga Kudu da Sani Mai Kifi daga Arewa.

Mohammed Abdu ne ya hada rahoton

Sauran dambatawar da aka yi Bahagon Dan Sama'ila daga Kudu ya buge Autan Nuran Dogon Sani daga Arewa a turmin farko.

Shagon Bahagon Na Bacirawa daga Arewa ya buge Shagon Dogon Jafaru daga Kudu a turmi na biyu.

Dogon Aleka daga Kudu ya doke Garkuwan Mutanen Karmu daga Arewa, sai karawar da aka yi canjaras tsakanin Shagon Ebola daga Kudu da Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa.

Sauran wasannin da aka yi canjaras Nokiyar Dogon Sani daga Arewa da Dogon Aleka daga Kudu.

Garkuwan Kwabre daga Arewa da Bahagon Dan Kanawa daga Kudu ma canjaras suka tashi da karawa tsakanin Shagon Fanteka daga Kudu da Shagon Aminun Langa-Landa daga Arewa.