Ban manta sunan sojan America ba – Trump

Myeshia Johnson Hakkin mallakar hoto Getty Images

Uwargidan sojan Amurkan da aka kashe a wani harin kwantan bauna a Nijar ta ce Shugaba Donald Trump ya kasa tuna sunan mijin nata a yayin da yake mata ta'aziyya ta wayar tarho.

Amma nan take Shugaba Trump ya wallafa rashin yardarsa da wannan furucin na matar a shafinsa na Twitter.

Shugaba Trump ya kira matar mai suna Myeshia Johnson, wanda mijin nata, Saje La David Johnson na cikin sojojin Amurka hudu da 'yan wata kungiya mai alaka da kungiyar IS suka kashe ranar 4 ga watan Oktoba.

Matar ta fito a wani shirin gidan talabijin na ABC mai suna Good Morning America, inda ta ce "Lallai shugaban ya ce ai mijina ya san makomarsa da ya shiga aikin soji.

Wannan ne karo na farko da ta bayyana halin da take ciki a bainar jama'a dangane da mutuwar mijin nata mai shekara 25 da haihuwa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Uwargida Myeshia Johnson da 'ya'yan marigayi sojan Amurka - Ah'leeysa mai shekara 6, da La David Jr. mai shekara 2

Ta kara da cewa "Yadda ya bayyana lamarin da salon maganarsa sun fusata ni, kuma sai da nayi kuka."

Uwargida Myeshia Johnson wacce a halin yanzu take dauke da cikin dansu na uku ta bayyana cewa, "na ji shi yana kame-kame domin ya manta sunan mijina, kuma wannan abu ne da ya kona min rai fiye da komai."

Shi kuwa shugaba Trump, maida martani yayi a shafinsa na Twitter, inda ya ce: "Na tattauna cikin mutunci da matar marigayi Saje La David Johnson, kuma na fadi sunansa daga fari babu wata inda-inda!"

Wata 'yar majalisa ce, Frederica Wilson daga jihar Florida kuma 'yar jam'iyyar Demokrat ta fallasa bayanan tattaunawar da shugaba Trump yayi da matar marigayin, inda ta tuhume shi da rashin tausayawa matar.

Wannan batun ya janyo kace-na-ce tsakanin jami'an gwamnatin shugaba Trump da 'yar majalisa Wilson, kuma da alama tsugune bata kare ba.

Uwargida Myeshia Johnson ta fada wa tashar ABC cewa bayanan 'yar majalisa Wilson yayai daidai da ainihin abin da ya faru, wanda ke nuna cewa fadar shugaban Amurka tayi karya kenana game da batun.

Ta ce 'yar majalisar na tare da ita a lokacin da shugaba Trump ya yi mata wayar ta'aziyyar, kuma ta saurari tattaunawar daga farkonta har kashe.

Labarai masu alaka