Nigeria: Fursunoni za su yi zabe a 2019

A watan Fabrairun 2019 ne za'a gudanar da babban zabe a Najeriya. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A watan Fabrairun 2019 ne za'a gudanar da babban zabe a Najeriya.

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta ce tana duba yiwuwar kirkiro sabbin mazabu a gidajen yari da ke kasar.

Shugaban hukumar zaben Farfesa Mahmood Yakubu ya shaida wa wasu kungiyoyin farar hula a Abuja cewa, akwai wasu rukunoni na 'yan fursuna da za'a ba su damar kada kuri'a a zaben 2019.

Sai dai Farfesa Yakubu bai bayyana rukunonin fursunonin ba.

Akwai fiye da fursunoni dubu 68,000 da ake tsare da su a gidajen yari daban-dabam a fadin kasar.

Galibin fursunonin dai suna jira ne a yi musu shari'a.

Kungiyoyi da sauran masu fafutika a Najeriya sun dade suna matsin lamba ga hukumomi don su ba 'yan fursuna damar kada kuri'a.

A cewar kungiyoyin, rashin bai wa fursunoni damar yin zabe tamkar tauye hakkokinsu ne.

A watan Fabrairun 2019 ne za a gudanar da babban zabe a Najeriya.

Labarai masu alaka