Zaben Kenya na cike da takaddama

Kenya at the crossroads Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kotun koli ta Kenya na fuskantar jan aiki a gabanta. An shigar da wata kara a gaban alkalan kotun domin su fayyace ko ya kamata a cigaba da zaben shugaban kasar da aka shirya gudanarwa gobe.

Alkalan kuma sun amince su duba wani koke na gaggawa mai neman a jingine zaben ko ma a dakatar da shi gaba daya.

Shugaban gamayyar jam'iyyun adawa ta NASA, Raila Odinga ya fasa tsayawa a zaben, amma a daya bangaren shugaban kasar na cewa sai an gudanar da zaben ba tare da jinkiri ba.

Masu shigar da kara zasu iso kotun kolin nan ba da jimawa ba, domin su nemi ta dakatar da wannan zaben.

Za su kuma nemi a gudanar da wani sabon zaben, wanda zai iya daukar watanni kafin a shirya shi, kuma yana iya jefa kasar cikin rudanin tsarin mulki.

Harun Ndubi shi ne lauyan babban kotu da zai kawo wannan karar a kotun kolin.

"A madadin masu kara, mun shigar da koke a gaban kotun koli inda muke neman ta soke sabon zaben da aka shirya na 26 ga wata".

Ya kara da cewa: "Wadanda nake wakilta na cewa kamata yayi a gudanar da zaben mai inganci, wanda za a kamanta adalci, kuma wanda ya yi daidai da abin da dokar kasa ta tanada".

Mista Ndubi ya ce kamata yayi a soke zaben na gobe, idan babu adalci a cikinsa:

"Amma idan haka ba zai samu ba, to kamata yayi mu fasa gudanar da shi babu jinkiri, domin mu sami zabe wanda zai gamsar da dukkan 'yan Kenya su goyi bayan wanda yayi nasara a zaben".

Abin damuwa shi ne wannan yanayin ya zame tamkar taken dukkan zabubbuka a Kenya.

Rikice-rikce sai karuwa suke a biranen Nairobi da Kisumu - inda 'yan adawa suke da goyon baya a yammacin kasar, inda kuma ake ta kamfe ga mutanen yankin su kauracewa zaben.

Raila Odinga na da jerin dalilai da suka sa ya fice daga zaben: "Ba a samar da isassun sauye-sauyen da zasu tabbatar da zabe mai inganci ba".

Kotun kolin Kenyar zata yanke hukunci game da ko hukumar zabe zata iya cigab da gudanar da zaben.

An dai kawo kuri'u, kuma wani kamfanin Faransa da ke da alhakin bayyana sakamakon zaben ya ce ya shirya tsaf.

Abin mamaki na baya-bayan nana shi ne cewa a makon jiya shi kansa shugaban hukumar zaben, Wafula Chebukati ya nuna shakku game da zaben.

"A irin wannan yanayin, da wuya a iya tabbatar da zabe mai inganci", inji shi.

Rudanin bai tsaya anan ba, domin daya daga cikin kwamishinoninsa ta tsere zuwa Amurka.

Roselyne Akombe ta ce tana tsoron abin da zai iya faruwa a gareta, kuma tana da shakku game da zaben...

Kwatsam sai shima shugaban hukumar zaben yace zai tafi hutu, kuma ya janye kansa daga gudanar da zaben.

Da alama dai rarrabuwar kawuna da rigingimu ba zasu sa mutane su amince da hukumar zaben ba.

Ana kusa da daina gangamin neman kuri'u, sai shugaba mai ci Uhuru Kenyatta ya bayyana cewa dole ne a gudanar da wannan zaben ba tare da jinkiri ba.

Shugaba Kenyatta ya ce: "Tattalin arzikin kasarmu na bukatar bunkasa, kuma dole ne mu kawar da wannan yanayi na rashin tabbas da muke ciki".

Shugaban ya kara da cewa: "Ina kira ga dukkan 'yan Kenya da fito ranar 26 ga watan Oktoba domin zaben dan takarar da suke ra'ayinsa".

A nasu bangaren, jakadun kasashen Turai sun ja hankalinsa da ya tyi taka tsantsan...sun yi kira ga 'yan siyasar kasar da su hau teburin tattaunawa.

Jakadan Amurka, Bob Godec ya bayyana matsayin kasashen duniya.

Ya kamata 'yan Kenya, musamman 'yan siyasar kasar su yi taka-tsatsan, kada su ruguza abin da aka shafe shekaru masu yawa wajen ginawa".

Ana sauran kwana daya a fara zaben, har yanzu 'yan kasar basu da tabbacin ko za a gudanar da zaben shugaban kasar.

Kuma idan anyi zaben, ko jerin kararraki a gaban kotuna da zasu biyo bayan zasu sa a karbe shi da hannu bibiyu. Tambaya anan ita ce: Shin, tsarin demokradiyyar Kenya zai iaya jure wa abin da zai biyo baya kuwa?

Labarai masu alaka