Ko Facebook na satar jin hirarrakinmu?

Mutane da dama Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mutane da dama sun ce suna jin Facebook na satar hirarrakinsu ta waya

Ko da yaushe Facebook yana musanta amfani da 'yan kananan lasifikokin wayoyin zamani wajen tattara muryoyi daga hirarrakin jama'a, daga nan sai ya yi amfani da irin wadannan bayanai don aika musu tallace-tallace.

Makon jiya mataimakin shugaban Facebook mai kula da harkokin talla, Rob Goldman, ya fada a sakon Twitter cewa katafaren kamfanin fasahar ba ya yi, kuma bai taba yi ba.

"Kawai ba gaskiya ne ba," ya fada a Tiwita.

Bisa la'akari da adadin tallace-tallacen intanet da mutane ke gani a kullum, akwai wata gagarumar mujadala, cewa tsagwaron arashi ne - watakila an sanya tallace-tallacen tun tuni, ba kuma tare da an lura da su ba, sai yanzu kawai hankali ya zo kansu.

Sai dai, akwai mutanen da sun yi yakinin cewa hakan ta faru a kansu. Ga irin labaran da wasu suka bayyana wa BBC.

Mun ga tallar bukukuwan aure kafin mu bayyana sa ranarmu

"Ni da wadda aka yi mana baiko sun samu tallace-tallace kan bukukuwan aure kwana guda bayan mun tsaida rana, tun kafin mu kai ga fada wa kowa," a cewar Nate, daga Springfield, a Amurka.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mun sayi zoben baiko bayan ganin tallarsa a intanet

"Cikin garaje muka sayi zoben sa rana ba tare da mun yi la'akari da wani abu mai alaka da haka ba.

"Duk da yake mako biyu a baya ni da ita mun je gidan wani abokinmu, muka sha barasa, wadda ba mu taba saya ko yin maganarta ba a wayar tarho.

Amma kwatsam da safe tallanta ne ya fara bayyana lokacin da ta bude shafinta na Facebook."

Na'urar taimaka wa jina tana sadarwa da wayata

"A shekara ta 2016, Kunnena na dama ya daina ji. Sai aka ba ni wata 'yar na'urar taimaka wa ji wadda ake hada ta da iPhone," Jon a Amurka ya ce.

"Hakan ta sa ina iya amsa waya, na saurari kida da sauransu ta hanyar wannan sabuwar na'ura.

"Duk lokacin da na hada wayata da na'urar kara jin, nakan ji wani canji, kamar wata 'yar kara dil, saboda za ta sauya karakainar da take yi daga duniyar da ke zagaye da ni zuwa sautin da take ji daga na'urar nan.

"A manhajar Facebook Masinja da ma shafina na Facebook duka, ina jin irin wannan 'yar kara, wato wayar ta sauya akalarta daga na'urar kara jina.

An yi haka lokaci ya fi a kirga, kai ko da na kashe muryar wadannan manhajojin."

Na samu wani talla kan aikin da na ambata cikin raha

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Cikin raha na ambata samun aiki a kamfanin sarrafa kofi

"Kawai makon jiya na dakatar da aikina kuma na zauna da kawata muna hira a kan abin da zan yi nan gaba," Lindsey daga Lincoln ta bayyana.

"Sai na ce, 'Ai ko ina son shan kofi, Mai yiwuwa na tsinci kaina a kamfanin Starbucks, yadda zan rika shan kofi sosai.'

"Karo na gaba da na leka shafina na Facebook a kan wayata, [Sai na ga] wani tallar kamfanin sarrafa kofi na Starbucks, inda suke wani taro a London don neman sabbin ma'aikata."

Kwatsam mun ga rumfar ajiye kwandunan shara bayan hirar

"Kwanan nan na samu wani talla da ake tura wa mutum, kuma ya ba ni mamaki matuka har na kasa nutsuwa, kai abin ya fi karfin arashi, bayan na yi kira ta manhajar WhatsApp," a cewar Olivia, daga Austin.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Akwatin ajiye kwanduna zuba shara

"Ina cikin tafiya da kawata wadda ke zaune a London inda take fada min wani labari kan yadda sabon mai gidan hayarsu ya sayo wata rumfa da ake kafawa a waje don ajiye kwandunan shara."

"Muka yi ta dariya a kan haka, har nake bayyana mata yadda ni ma nake bukatar irin wannan abu a nan Texas.

"Washe gari kawai ina bibiyar labaran Facebook dina, ba sai na ga wani talla daga kamfanin Wayfair mai sayar da kayan amfanin gida ba.

Ana nuna mini wata rumfa ta ajiye kwandunan zuba shara, abin nan ya yi matukar ba ni mamaki.

"Kafin mu yi waccan hira, ban taba sanin da irin wannan rumfa ba a duniya."

Cikin minti biyar sai ga talla biyu na katifa

"Muna ta muhawara kan wannan abu, ni da wasu abokaina a gidan barasa... don gano gaskiya kuma a raba musu, sai muka shiga tattauna batun sabuwar katifa," in ji Justin, a Atlanta.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mun shiga hirar katifa don gano gaskiyar wannan batu

"Tun da yake ban taba saya ko neman saya, kai ko na yi tunani game da gado ba.

Na shafe shekaru da dama, don haka ba zan ma iya tuna wani lokaci da na ga tallar katifa a intanet ba.

Muka fara hira a kan gadaje da katifu muna ambaton kalmomi, irinsu birgima a kan wani gado da ake kira 'California king' da 'sayen katifa ta intanet' a hirar, a lokacin da muke bibiyar shafukanmu na facebook.

"A cikin minti biyar sai ga talla biyu na katifu. Ba mu taba ganinsu ba kafin hirar."

Talla cikin harshen Sifaniyanci ya bayyana

"Ina aiki a masana'antar wayoyin salula kuma na lura da yadda hakan ke faruwa sau da dama a cikin 'yan shekarun nan," Michael, daga Grimsby ya rubuta.

"Don in tabbatar, sai na fara koyon harshen Sifaniyanci, kuma cikin kwana daya sai ga tallace-tallacen kayayyaki cikin harshen Sifaniyanci! Wallahi hankali ba zai dauka ba."

An yi mini talla kan kyamarorin tsaron gida

"Na kai wa wata kawata da ke kafa kyamarorin tsaro ziyara a gidanta," Melissa, daga Australia, ta rubuta.

"Ban taba amfani da intanet don neman wani abu mai alaka da tsaron gida daga nesa ba, amma kasa da sa'a daya bayan hirarmu kan yadda ake kafa kyamarorin, sai na samu tallar kyamarorin tsaron gida a Facebook.

"Duk tsawon lokacin hirarmu wayata tana cikin aljihuna."

Na samu tallace-tallace kan aikin ido duk da yake idanuna garau

"Wata rana, wani abokina ya fada min bukatar da yake da ita, ta a yi masa tiyata a ido," in ji Austin, daga Tigard, a Oregon.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Daga zancen aikin ido sai ga tallar ta bayyana a Facebook

"Kawai bayan nan, Ina bincika Facebook dina sai na ga tallar irin wannan tiyata da ake kira Lasik.

"Ni idona garau yake, ban taba neman bayani a kan tiyatar Lasik ba."

Sai na ga bindigar kashe kuda da ban taba gani ba

"Na ga wani abu a makaranta da ake kira bindigar gishiri, wadda ake amfani da ita wajen kashe kudaje," a cewar Peter, "ban taba ganinta ba sai lokaci, kuma ban taba bincika irin wadannan abubuwa ba.

"Muna hira da matata sai zancen bindigar ya fado, nake bayyana mata wadda na gani.

"Washe gari da safe, ina bude Facebook dina sai ga talla daga kamfanin Amazon na irin wannan bindiga a cikin jerin 'abubuwan da mai yiwuwa kake da sha'awa'."

Ta faru da ni ba sau daya ba

"Hakan ya faru da ni, karo da dama ina ganin tallace-tallace masu alaka da wata hira da na yi ko na gama yi kenana," Faris, daga Alkahira ya ce.

"Mun yi hira a kan abokin dan'uwana da ya mutu, kuma ba da dadewa ba sai daya daga cikinmu ya ga tallace-tallace a kan masu shirya gawa.