'Wata 2 ina kitsa harin New York' - Saipov

Sayfullo Saipov - wanda ake tuhuma da kai harin birnin New York

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sayfullo Saipov

Kwana daya bayan mummunan harin birnin New York a yankin Lower Manhattan, hukumomi a Amurka sun gurfanar da mutumin da suke tuhuma da kai harin, a gaban wata kotu a Amurka.

Ana tuhumar Saifullo Saipov da bai wa kungiyar IS goyon baya, da kuma kashe mutum takwas.

Kuma jami'an shari'a sun ce Saipov, wanda dan asalin kasar Uzbekistan ne zai fuskanci hukunci mai tsanani.

Saipov ya ce baya bukatar kariyar da doka ta ba shi na kin cewa uffan har sai an kai shi gaban alkali, domin ya rika amsa tambayoyi tun yana bisa gadon asibiti. Jami'an 'yan sanda sun nemi su ji dalilinsa na kai hari mafi mumi a New York tun na Satumba 2011.

Asalin hoton, Getty Images

Da farko dai shi Saipov, mai shekara 29 ba ya cikin jadawalin masu alaka da kungiyoyin 'yan ta'adda.

Kuma ya fada wa 'yan sanda cewa tun wata biyu da suka gabata ya kitsa kai harin ta amfani da mota, a wannan lokaci na bikin Halloween domin tutunan birnin zasu kasance makil da jama'a.

Hukumomi sun gano bidiyon kungiyar IS guda 90 a cikin wayarsa ta hannu. Sun kuma ga wata wasika a cikin motarsa, wacce aka rubuta ta da Larabci inda suka ga wani sakon IS mai cewa daular Islama zata dore har abada.

Ryan Nash shi ne dan sanda na farko da ya fara tunkarar Saipov bayan da ya fice daga cikin motarsa, yana rike da wasu bindigogi na bogi. Ya ce dakatar da Saipov ne ke zuciyarsa, ba neman suna ba:

"Na san an yaba da abin da nayi, amma aikina kawai nake yi".

Kalaman na dan sanda Nash sun biyo bayan tarin yabon da ya sha domin rawar da ya taka wajen kama mutumin a maimakon harbe shi har lahira.

Ana nan ana cigaba da bincike, amma 'yan sanda sun cire shingayen da suka saka a wurin da harin ya auku.

Magajin garin New York, Bill De Blasion ya yi kira ga mutanen birnin New York da su zama cikin shirin ko ta kwana, amma kada su razana.