Ana yunkurin hana biyan sadaki a Zimbabwe

Al'adu da dama a kasashen duniya sun amince da biyan sadaki. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Al'adu da dama a kasashen duniya sun amince da biyan sadaki

Wata lauya a Zimbabwe ta shigar da kara a gaban kotu domin kalubalantar tsarin biyan sadaki da ake kira Iobola , wanda ta bayyana a matsayin tsohuwar al'ada wadda ta rage kimar mata a cewar jaridar Herald.

Priccilar Vengesai ta yi ammanar cewa , idan aka ci gaba da amfani da wannan al'ada, toh ya kamata iyalan amarya da na ango kowanensu ya dauki nauyin biyan sadaki domin daidaita tsakanin jinsi.

Ta shigar da kara a gaban kotun kudin tsarin mulkin Zimbabwe inda ta nemi kotun kan ta fayyace mata a kan ko tsarin ya sabawa hakkinta na zama yar kasa.

Jaridar ta ambato Ms Vengesai na cewa tana son ta sake aure , kuma bata son ta sake fuskantar matsalar, irin wadda ta kunno kai a auren da ta yi a baya.

Ta ce ba bu rawar da ta takawa la okacin da aka bayyana kudin sakinta.

Ta kuma kara da cewa baa bata damar tambayar ko nawa ne aka biya a matsayin sadakinta ba.

Ms Vengesai ta ce lamarin ya sa ta rika ji kamar an mayar da ita wata kaddara, da kawunta da kuma mijinta suka kayyade kudin da zaa biyata.

Ta ce wannan ya shafeta matuka kuma ya sa ta kasance karkashin ikon mijinta saboda tana ji kamar sayanta ya yi.

"Ni yar kabilar Shona ce kuma ina da anniyar ganin cewa na sake yin wani aure nan bada jimawa ba, da zarar an shawo kan wannan batu".

A karkashin al'adar ta Shona, ana bukatar a biya sadakin mace kafin iyalinta da kuma sauran alumma su amince da aurenta.

A lamuran da ba a biya sadaki ba, iyaye da 'yan uwan amarya ba za su amince a daura mata aure da angonta ba karkashin dokar yin aure ta kasar.