Abin da ya sa na yi wa Buhari uzuri – Soyinka

  • Latsa alamar lasifika dake sama don sauraron ganawar da farfesan ya yi da BBC.

Farfesa Wole Soyinka ya ce Shugaba Najeriya, Muhammadu Buhari ya yi kokari a fannin cin hanci da rashawa da kuma batun yaki da Boko Haram.

Sai dai ya ce zai so ya ga shugaban ya daure wadansu mutane kan laifin cin hanci da rashawa.

Farfesan mutum ne wanda ya yi suna wajen fafutikar kare tsarin dimokradiyya.

A baya mutum ne da yake yawan sukar shugabannin mulkin soji; kuma ya sha shiga zanga-zangar adawa da gwamnati.

A wannan makon mun kawo muku kashi na farko na hira da Farfesan wanda Jimeh Saleh, Editan sashen Hausa na BBC, ya yi da shi a ofishinmu na Landan.

Ku kasance da mu a mako mai zuwa don sauraron ci gaban hirar.

Karanta wadansu karin labarai ba