'Har yanzu talaka na cikin wahala a Nigeria '

Wasu 'yan Nigeria na ci gaba da kokawa game da matsin rayuwa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wasu 'yan Nigeria na ci gaba da kokawa game da matsin rayuwa

Manoma a Nigeria na ci gaba da girbin amfanin gona a yankunan karkara, musamman ma a arewacin kasar.

Duk da cewa manoma da dama na cewa damina ta yi albarka, wasu kuma kuka suke yi, suna cewa abin da suka noma ba zai ciyar da iyalansu ba, sakamakon matsin rayuwa.

Sun ce yanayin da suke a yanzu ya banbanta dana a baya, kuma suna fuskantar matsaloli na rashin babu.

Mutanen da suka fito daga yankin sabon rafi da ke jihar Katsina sun nemi gwamnati akan ta taimaka mu su da sana'oi.

Hukumomi a Najeriya sun dinga ikirarin cewa kasar ta fita daga durkshewar tattalin arziki.

Sai dai har yanzu jama'a na da dama na ci gaba da kokawa game da yanayi na ha'u'la'i da suka shiga sakamakon rashin aikin yi da kuma kudi.