Nigeria: Buhari ya gabatar da kasafin kudin 2018 na N8.6tr

Buhari da Bukola da Dogara
Image caption Wannan ne kasafin kudi na uku da shugaban Najeriyar ya gabatar ga majalisar dokokin kasar tun bayan ya hau karagar mulki a shekarar 2015

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin kasar da ya kai naira tiriliyan 8.6 ga majalisar dokokin kasar.

A jawabinsa ga majalisar dokin kasar yayin gabatar da kasafin, Shugaba Buhari ya ce gwamantinsa tana tsammanin za ta samu kimanin naira tiriliyan 2.442 daga albarkatun mai.

Ya kara da cewa Najeriya tana hasashen cewa za ta sayar da gangar mai sama da miliyan biyu a ko wacce rana.

Shugaba Buhari ya ce gwamnati za ta kashe naira biliyon 300 kan gyara hanyoyi a fadin Najeriya.

Muhammadu Buhari ya ce gwmnatinsa za ta ware naira biliyon 8.9 domin tahsar samar da wutar lantarki ta Mabila .

Yaya aka kashe kasafin 2017?

Hakkin mallakar hoto Nigeria presidency
Image caption Shugaba Buhari ya ce yana son inganta rayuwar al'umma ta hanyar kasafin kasa

Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta samu ta yi hanyoyin kwalta na sama da kilomita 766 a fadin kasar a kasafin kudin shekarar 2017.

Shugaban ya ce ba ya ga inganta harkokin noma da samar da makamashi, gwamnatinsa ta mayar da hankali ne kan biyan basussukan ayyukan da gwamnatocin baya suka bari ga 'yan kwangila domin a kammala ayyukan samar da ababen more rayuwa a kasar.

Ya bukaci 'yan Najeriya da su kwana da tabbacin cewa gwamnatin kasar tana iya abin za ta iya yi domin ta samar da dauwamammiyar wutar lantarki ga 'yan kasar.

Labarai masu alaka