Daura Fura Delicacy Disco
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Me mutanen Daura ke fadi kan mulkin shugaba Muhammadu Buhari?

A Najeriya, kusan kowace al`uma tana da abincin da ta shahara da shi. To ko kun san cimar mutanen Daura, wato mahaifar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari?

Ibrahim Isa ya ziyarci unguwar Kwari, kusa da rijiyar Kusugu mai dadadden tarihi a birnin Daura, inda ya bige da tattaunawa da wasu Daurawan suna dibar damun fura, inda ya fara da tambayarsu matsayin ta a wurin su da kuma gajiyar da suka ci daga gwamnatin da dansu ke jagoranta bayan shi ma ya dirki fura da nono.

Sai ku latsa alamar lasifika dake sama domin sauraron cikakken rahoton na Ibrahim Isa.

Image caption Ibrahim Isa a yayin da yake diban furarsa a birnin Daura