An samu gibin amfanin gona a Damagaram

Fadama
Image caption Manonan rani a Niger

An samu tangarda a damunar bana ta fuskar amfanin gona a wasu yankunan jihar Damagaram ta Jamhuriyar Nijar.

Gwamnatin kasar ta bayyana sakamakon wucin gadi na damunar da ta gabata game da halin da jihar ke ciki.

An samun babban gibi a amfanin da aka girbe a wasu garuruwa na jihar, gibin da ya kai kashi 50 cikin 100.

Karamin minista a ma'aikatar noma da kiwo, Mohamed Busha shi ya bayyana haka bayan wani rangadi da ya kai jihar ta Damagaram.

Ya kuma ce "cikin garuruwa 3, 378 wasu 502 daga ciki ba su samu cimaka yadda ya kamata ba".

Niger ta nemi taimakon Amurka

Niger : Ambaliyar ruwa ta yi barna a Yamai

Niger: Manoma da makiyaya na samun horo kan zaman lafiya

Image caption Makiyaya a Niger

Kashi 15 cikin 100 na manoman kauyukan jihar ne damuna ta kayar da su saboda kamfar ruwan sama da aka samu.

Haka ma lamarin ya kasance ta bangaren abincin dabbobi.

Sai dai kuma, wutar daji na daya daga cikin barazanar da abin da aka samu na abincin dabbobin ke ci gaba da fuskanta a yanzu haka.

Bayan damuna, an samu wutar daji har sau 21 a cikin jihar, abin da ya haddasa konewar eka 4, 180 kunshe da abincin dabbobi.

Labarai masu alaka