Dakarun soja sun kwace iko a Zimbabwe

Zimbabwean Army Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An cusgunawa wasu ma'aikatan gidan talbijin din lokacin da sojoji suka mamaye tashar

Shafin Tiwita na jam'iyyar Zanu PF ya yi ikirarin cewa an nada Emmerson Mnangagwa a matsayin shugaban riko a kasar.

An kori Mista Mnangagwa mai shekara 75 ne daga kan mukaminsa na mataimakin shugaban kasa kan abin da gwamnati ta kira "halayyar rashin biyayya".

Jam'iyyar Zanu-PF mai mulki ta musanta yin juyin mulki, amma dai ta ce an samu wani "sauyin da babu zubar da jini" na mulki.

Sojoji a Zimbabwe sun kwace iko da gidan talbijin din gwamnatin kasar inda suka sanar da aniyar kama makusantan Shugaba Mugabe.

A cewarsu jami'an ne suka janyo matsin rayuwa da na tattalin arziki a kasar.

Wani Janar cikin kakin soja ya musanta cewa matakin salon juyin mulki ne bayan an ji rugugin bindigogi da fashe-fashe a birnin Harare.

Matakin sojojin ya zo ne bayan Shugaba Mugabe ya kori Mataimakinsa Emmerson Mnangagwa, a wani rikici kan gadon mulkin kasar.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani babban abokin adawar Robert Mugabe ya ce ya yi imanin ikirarin sojojin cewa ba juyin mulkin suka yi ba, ba gaskiya ba ne

A jawabinsa na minti biyar, Manjo Janar SibuSuso Moyo ya ce Shugaba Mugabe da iyalinsa na nan lafiya.

"Muna son ba wa al'ummar kasa tabbacin cewa Shugaban Jamhuriyyar Zimbabwe kuma babban kwamandan rundunar tsaron kasar, Robert Mugabe da iyalinsa na nan cikin koshin lafiya kuma akwai tabbacin tsaronsu."

Wasu rahotanni da ba a tabbatar ba na cewa an kama akalla minista guda da kuma babban sufeton 'yan sandan Zimbabwe.

Cikin dare an ji amon harba manyan bindigogi da atilare a yankunan arewacin birnin Harare.

Sojojin suka ce suna son su yi maganin wadanda "ke tafka aika-aikar da ta tsunduma kasar cikin wahalar rayuwa da matsin tattalin arziki.

"Kuma da zarar mun kammala aikinmu, muna sa ran cewa harkoki za su koma kamar yadda aka saba."

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An cusgunawa wasu ma'aikatan gidan talbijin din lokacin da sojoji suka mamaye tashar

An ga motoci masu sulke a kusa da tsakiyar birni. Tun da farko, jakadan Zimbabwe a Afirka ta Kudu, Isaac Moyo ya yi watsi da rade-radin juyin mulki, ya ce har yanzu gwamnati "na nan lafiya".

A ranar Talata ce jam'iyyar Zanu-PF ta Zimbabwe ta zargi babban hafsan sojin kasar da tunzura bore bayan ya ce rundunar soja a shirye take ta shiga tsakani don kawo karshen rikicin siyasa.

Wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar na bayyana kalaman Janar Constantino Chiwenga a matsayin wani abin mamaki da firgitarwa kuma cin amanar kasa.

Babu dai wani martani daga bakin shugaban Zimbabwe, Robert Mugabe dan shekara 93 a duniya.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Babban hafsan sojin Zimbabwe Janar Constantino ya yi gargadin cewa sojoji na iya kwace iko

Janar Constantino Chiwenga ya kalubalanci Shugaba Mugabe bayan ya kori mataimakinsa daga kan mukaminsa.

Sojoji sun fada wa ma'aikata a tashar yada labaran gwamnatin kasar cewa "kada su damu", wata majiya ta kara da cewa, kuma sun je ne kawai don su kare ginin.

Wakiliyar BBC a Harare Shingai Nyoka, ta ce an ji amon manyan bindigogi da atilare a unguwannin arewacin birnin, inda wasu manyan jami'an gwamnati ciki har da shugaban kasar ke da zama.

Ofishin jakadancin Amurka a Harare ya aika wani sakon tiwita cewa "saboda rashin tabbas din da ake ciki" ba zai bude ba ranar Laraba.

Ya kuma shawarci Amurkawan da ke Zimbabwe su "nemi wurin fakewa" har zuwa lokacin da za su ji sanarwa ta gaba.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce tana "bibiya kut-da-kut" halin da aka shiga a Zimbabwe kuma ta bukaci dukkan bangarori su warware dambarwarsu cikin "lumana da kwaciyar hankali".

Labarai masu alaka