Ana gwanjon bayi a Libya

Bukatar hakan ta taso ne bayan da gidan talibijin na CNN ya nuna aka sayar da wasu matasa bakar fata Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Bukatar hakan ta taso ne bayan da gidan talibijin na CNN ya nuna aka sayar da wasu matasa bakar fata

Kungiyar tarayyar Afirka ta yi kira ga mahukuntan Libya da su yi bincike akan gwanjon bayi da ake yi a kasar.

Bukatar hakan ta taso ne bayan da gidan talabijin na CNN ya nuna wasu hotuna da ke nuna yadda ake sayar da matasa bakar fata ga wasu mutane daga kasashen Arewacin Afirka a matsayin manoma wanda wasu ake sayar da su akan dala 400.

Hotunan dai wata shaida ce ta baya bayan nan da ke nuna cewa ana cin zarafin 'yan ci rani wadanda ke kokarin tsallakawa zuwa nahiyar turai ta Libya.

Hukumomi sun ce 'yan cirani fiye da 250 ne da ke kan hanyarsu ta zuwa Spaniya a cikin wasu kananan jiragen ruwa aka ceto a tekun baha-rum a ranar Juma'a.

A yan watannin baya bayanan ,ana samun karin mutane da ke kauracema Libya saboda ana cin zarafinsu, a yanzu sun maida hankali ne kan kasar Morocco.

Labarai masu alaka