Alex Ekwueme ya rasu

Marigayin ya rasu ne a birnin Landan inda ake yi masa jinya Hakkin mallakar hoto DAILY TRUST
Image caption Marigayin ya rasu ne a birnin Landan inda ake yi masa jinya

Rahotanni sun ce tsohon mataimakin shugaban kasar Nigeria, Dr Alex Ifeanyichukwu Ekwueme ya rasu.

Ya rasu ne yana da shekara 85 a duniya.

Dan uwansa wanda shi ne sarkin Oko a jihar Anambra, Igwe Laz Ekwueme ya ce marigayin ya rasu ne da misalin karfe 10 na daren Lahadi a wani asibiti da ke birnin Landan.

Marigayin wanda mai tsara gine -gine ne , ya kasance dan Najeriya na farko da aka zaba a matsayin mataimakin shugaban kasa daga shekarar 1979 zuwa 1983.

Ya dai fadi ne a gidansa da ke Enugu kuma cikin gaggawa aka tafi da shi wani asibiti da ke birnin Enugu inda ya shiga cikin wani yanayi na doguwar suma.

Daga bisani kuma aka wuce da shi birnin Landan .

Ekweme dai shi ne tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Shehu Shagari wanda aka hambarar da gwamnatinsa a juyin mulki da sojoji suka yi a shekarar 1984 a karkashin jagoranci shugaba Muhamadu Buhari wanda a lokacin babban janarar ne a rundunar sojin Nigeria.