'Yan Zimbabwe na tururuwa don rantsar da Mnangagwa

Zimbabweans Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dumbin 'yan kasar ne suka fita kan tituna suna murnar sauka daga mulkin Mugabe

Dubban 'yan Zimbabwe ne ke tururuwa zuwa filin wasa na Harare, babban birnin kasar don shaida rantsuwar tsohon ministan tsaron kasar mai shekara 75, Emmerson Mnangagwa da ake yi wa lakabi da "Kada".

Emmerson Mnangagwa na maye gurbin Robert Mugabe wanda ya shafe tsawon shekara 37 a kan karagar mulkin kasar Zimbabwe.

Ba lallai ne tsohon shugaban kasar ya halarci bikin rantsar da magajin nasa ba, wanda tun bayan saukarsa mulki sakamakon matsin lamba daga sojoji ba a gan shi a bainar jama'a ba, .

Sojojin kasar sun dauki matakin goya wa Mnangagwa baya ne lokacin da aka kore shi daga mukamin mataimakin shugaban kasa yayin wata gwagwarmayar iko da tsagin da ke biyayya ga Grace, matar Robert Mugabe.

Mista Mugabe da Mnangagwa sun yi aiki kafada da kafada tun lokacin gwagwarmayar kwatar 'yanci daga 'yan mulkin mallaka a shekarun 1970.

Kungiyar Raya Kasashen Kudancin Afirka ta ce a shirye take ta yi aiki kut-da-kut da sabon jagoran Zimbabwe.

Labarai masu alaka