Tafkin Victoria na fuskantar barazana

Tafkin Victoria shi ne tafkin ruwan dadi mafi girma a nahiyar Afrik, mai iyaka da kasashen Uganda da Kenya da Tanzani Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tafkin Victoria shi ne tafkin ruwan dadi mafi girma a nahiyar Afrik, mai iyaka da kasashen Uganda da Kenya da Tanzani

Masana kimiyya na gargadin cewa tafkin Victoria ,wanda shi ne tafkin ruwan dadi mafi girma a nahiyar Afrika , na fuskantar barazanar gurbacewa.

Tafkin Victoria shi ne tafkin ruwan dadi mafi girma a nahiyar Afrika, mai iyaka da kasashen Uganda da Kenya da Tanzania

Sun ce yawan kamun kifi da ya zarce kima tare da gurbatar muhalli ya kassara adadin kifayen da ake samu a cikinsa, abinda ke barazana ga rayuwar miliyoyin masuntan da suka dogara da tafkin.

Masanan sun ce gurbataccen ruwan dake kwarara cikin tafkin na haddasa dafi a cikinsa, yayinda takin da ke gangarowa daga gonaki ke kashe tsirran da ke rayuwa a cikin ruwan.

Kuwesi Edi na daya daga cikin masuntan da ke kamun kifi a tafkin kuma ya ce kifin da suke kamawa ya yi karancin kwarai.

Ya baya wuce kilo goma kuma a da su kan kama kifi kilo dari zuwa dari biyar.

Kuwesi ya ce yana matukar fargabar abinda zai faru nan gaba.