An ware ranar tuna haihuwar Mugabe a matsayin hutu a Zimbabwe

Robert Mugabe Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mista Mugabe ya mulki Zimbabwe tun lokacin da ta samu 'yancin kai a shekarar 1980

Gwamnatin Zimbabwe ta ayyana ranar tunawa da haihuwar hambararren shugaban kasar Robet Mugabe, a matsayin ranar hutu a ko wcace shekara, don nuna girmamawa gare shi na gudunmuwar da bayar wajen gina kasar.

Jaridar Herald ta kasar ta ruwaito cewa, gwamnatin ta dauki wannan mataki ne a ranar Juma'a bayan da sabon shugaban kasar Emmerson Mnangagwa ya sha rantsuwar kama mulki.

An dai ware ranar 21 ga watan Fabrairun ko wacce shekara ce a matsayin ranar hutu don girmama Mista Mugabe.

A watan Agustar da ya gabata ne gwamnatin Mista Mugabe ta yanke shawarar ware ranar tunawa da haihuwarsa a matsayin ranar hutu a kasar, sakamakon yawan kamun kafa da kungiyar matasa ta jam'iyyar Zanu-PF mai mulki ta dinga yi.

A makon da ya gabata ne sojojin kasar da kuma jam'iyyarsa ta Zanu-PF suka tursasawa Mista Mugabe sauka daga mulki.

Tarihin rayuwar Robert Mugabe a takaice

  • 1924: Shekarar da aka haife shi
  • An horar da shi a matsayin malami
  • 1964: Gwamnatin Rhodesia ta daure shi
  • 1980: Ya lashe zaben da aka yi bayan 'yancin kai
  • 1996: Ya auri Grace Marufu
  • 2000: Bai yi nasara ba a zaben raba-gardamr da aka yi ba na karfin ikon shugaban kasa da kuma hana Turawa mallakar gonaki
  • 2008: Ya zo na biyu a zagayen farko na zaben da suka fafata da Tsvangirai, wanda ya janye saboda harin da aka kai kan magoya bayansa
  • 2009: Ya rantsar da Tsvangirai a matsayin firai minista a lokacin da ake fuskantar durkushewar tattalin arziki a kasar
  • 2016: An gabatar da takardun lamuni a yayin da karancin takardun kudya yi tsanani
  • 2017: Ya kori mataimakinsa da ya dade suna aiki tare wato Emmerson Mnangagwa

Labarai masu alaka