Manoman alkama sun ce gwiwarsu ta yi sanyi da gwamnatin Buhari

Gona na bunkasa
Image caption Gonar alkama

Manoman alkama a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, sun fara yanke-kauna game da shirin gwamnatin tarayya na bunkasa noman alkama.

Manoman sun ce ba su taba samun tallafi daga hukumomin tarayya ba, duk da ikirarin gwamnatin Buhari na wadata kasa da abinci.

Masu noman na cewa, sai manomi ya je kasuwa da buhu 10 amma sai ya shafe sati guda bai sayar da ko buhu daya ba.

Bayan gwamnati ta yi kira ga manoman alkama su fadada noman, shugaban manoman alkama na jihar Kano, Alhaji Faruk Rabi'u Mudi ya ce daga manoma 800 har sai da aka samu 7, 000 da suka yi rijista.

A bara kawai sai da manoman alkama suka kai sama da dubu 30 a fadin jihar Kano, in ji shi.

Saboda matsaloli daban -daban da manoman alkamar ke fuskanta a jihar ta Kano a bana yawan wadanda za su noma alkama ya yi matukar raguwa zuwa kasa da dubu bakwai

A yanzu dai ana sayar da kwanon alkama daya a kan naira dari hudu, wanda a bara ana sayar da kwano daya ne a kan kimanin naira dubu daya.

Manoman sun yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shigo cikin wannan lamari na noman alkama.

Labarai masu alaka