Majalisar Dinkin Duniya 'ta yi wa dan Nigeria coge'

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Korafin Zanna Mustafa kan MDD

Wani Lauya dan Najeriya da ya lashe lambar yabo mafi girma da Majalisar Dinkin Duniya ke bayar wa kan ayukkan jin kai, ya nuna damuwa kan jan kafar da ya ce hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar (UNHCR) ke yi wajen ba shi kudaden da ke tare da lambar yabon kimanin dala 150,000.

Zanna Mustafa dai ya samu lambar yabon ne kan kafa wata makaranta a jihar Borno da ya yi, inda ake bai wa yaran da rikicin Boko Haram ya mayar marayu ilimi da abinci kyauta.

Kuna iya latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron korafin da Zanna Mustafa ya yi.

Ku karanta karin wasu labarai: