'Bokaye na kashe masu cuta mai karya garkuwar jiki'

AIDS Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Uwar marayu masu fama da cuta mai karya garkuwar jikin ta ce tana karbar 'ya'yan da take riko ne bayan iyayensu sun yasar da su

Wata uwar marayu da ke rikon yara masu fama da cuta mai karya garkuwar jiki ta koka kan yadda wasu ke ci da gumin masu fama da cutar ta hanyar ba su magungunan jabu da kan janyo mutuwar irin wadannan marasa lafiya.

Ta ce Bokaye da Malaman tsibbu da Fasto-fasto na sanya wa wasu masu fama da cuta mai karya garkuwar jikin daina shan magungunan da ake ba su a asibiti, inda suke komawa amfani da na gargajiya wadanda kuma a karshe su kai su ga halaka.

Hajiya Aisha Usman wadda ita ma tana fama da cutar ta ce kula da yara masu cutar kanjamau na da irin nasa kalubale, musammam a wajen mutumin da ba shi da cutar.

A cewarta: "Mai daki shi ya san inda dakinsa ke yoyo. Idan mutum ba shi da cutar to yana iya mantawa da lokacin shan maganin yaran da yake riko, amma idan mai fama da cutar ne yake kula da su. To, lokacin da ya tashi shan maganinsa zai kiyaye da yaron da ke hannunsa."

Hajiya Aisha Usman na wannan jawabi ne ga BBC a wani bangare na ranar tunawa da masu cuta mai karya garkuwar jiki ta duniya.

Ranar ta 1 ga watan Disamba, an kebe ta ne don hada kan al'ummar duniya da nufin yaki da cutar da kuma nuna goyon baya ga mutanen da suka kamu da ita har ma da tunawa da wadanda ta zama ajalinsu.

Wani kiyasi ya ce akwai mutane kimanin miliyan 34 a duniya da ke fama da cuta mai karya garkuwar jiki.

Wasu fiye da miliyan 35 kuma sun mutu sakamakon cutar, abin da ya sa ta zama daya daga cikin annoba mafi ta'adi a tarihi.

Uwar marayun ta ce tana samun yaran da take riko ne bayan iyayensu sun yasar da su ko kuma idan an mutu an bar su.

Ta koka kan yadda ake samun karuwar nuna kyama da tsangwamar masu fama da cuta mai karya garkuwar jiki a tsakanin al'umma.

"To, wallahi abin da nake fuskanta kenan. Akwai kyama, akwai tsangwama. Yanzu yaran nan tun da suke tare da ni, ko 'yan'uwana ne na ce to zan kawo muku yawon sallah, sai a ce kar in zo."

Ta ce: "A duk garin Kaduna, wuri daya kawai yaran nan suka sani. Kai, hatta masu irin wannan cuta ba sa maraba da su."

Ba su san ko'ina ba, ba su san kowa ba ban da ni, a cewar Aisha Usman.

Ta koka kan yadda ake samun lafawa kan wayar da kai game da cuta mai karya garkuwar jiki, "an yi shiru, an daina ambaton HIV."

Labarai masu alaka