Nakasassu na fuskantar matsaloli a Nigeria

Nakasassun sun ce ilimi shi ne gishirin zaman duniya amma suna fuskantar karancin kayan karatu Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Nakasassun sun ce ilimi shi ne gishirin zaman duniya amma suna fuskantar karancin kayan karatu

A ware ranar 3 ga watan disemba ta kowace shekata a matsayin ranar nakasassu ko masu bukata ta musamman ta duniya.

Majalisar dinkin duniya ta kebe wannan rana don nazarin kalubalen da suke fuskanta, tare da samar da hanyoyin da za su ji dadin rayuwa kamar kowa.

Sai dai Malam Lawal Tasi`u Mashi wanda shi ne shugaban kungiyar kyautata jin dadin makafi ta jihar Katsina, ya sheadwa BBC cewa suna fuskantar kalubale da dama.

Ya ce ta bangaren ilimi suna fuskantar tsada dangane da abubuwan da suka shafi karatu.

Ya kuma ce wannan yana sosa mu su rai, musaman idan aka dubi cewa ilimi shi ne abinda duniya ta sa a gaba, wajan samun cigaba.

Malam Lawal ya kuma ce suna fuskantar matsalar wajan neman aure.

Amma ya ce sun tashi tsaye wajan ganin 'yayansu sun samu ilimin boko