Taron samar da mafita a kan gurbatar muhali

Zubar da robobi a cikin teku na cikin abubuwan da ke gurbata muhali
Image caption Zubar da robobi a cikin teku na cikin abubuwan da ke gurbata muhali

Ministocin muhalli daga kasashe 100 ne zasu hallara domin tattaunawa akan atsalar gurbatar muhalli a Nairobi babban birnin kasar Kenya.

Ministocin za su yi kokari su samar da mafita akan matsalar ta gurbatar muhalli.

Majalisar dinkin duniya ta ce mutum miliyan tara sun mutu a shekarar 2015 sakamakon cututtuka masu nasaba da gurbataciyyar iska da ruwan sha ko kuma fili ,inda rabinsu suka fito daga kasashen China da India.

Kafafen yadda labarai a kasashen duniya da dama sun rika magana akan matsalar gurbata muhali kuma gwamnatocin na cigabaa da fuskantar matsin lamba daga alumominsu wajan ganin sun dauki matakan tsaftacce muhali.

Majalisar Dinkin duniya dai na kokarin ganin cewa ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta amma kuma ana fuskantar tafiyar hawainiya dangane da matsayar da ake son kasashen duniya su cimma akan yadda zaa dakile ayuikan da ke janyo gurbata muhali.

Alal misali sinadrin dalma da ke cikin fenti na yi yin illa ga kwakwalwar bil'adama kuma Birtaniya ta yi kokarin ganin cewa ta hana amafani da sinadarina shekarar 1992, sai dai ana amfani da shi a kasashe masu tasowa da dama.

Sai dai kuma ana fuskantar tsaiko game da matakan da aka dauka akan yadda ake gurbata muhali ta iskar da ake shaka da ruwan sha da kuma robobin da ake zubarwa a cikin teku.

Hakan dai ya biyo bayan jinkirin da ake fuskanta daga wurin gwamnaotoccin kasashen duniya ya yin da suke ci gaba da nazari akan illar da wadannan abubuwa suke yi ma bagaren lafiya da muhali da kuma yadda tattalin arzikin yake bunkasa.