Gwamnatin Sokoto na shirin bunkasa ilimin boko a jihar

A cikin shekaru 2 da suka gabata ne gwamnati jihar Sakkwaton ta kafa dokar ta baci a bangaren ilimin jihar Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A cikin shekaru 2 da suka gabata ne gwamnati jihar Sakkwaton ta kafa dokar ta baci a bangaren ilimin jihar

Gwamnatin jihar Sakkwato ta kudiri anniyar kafa cibiyoyin karatu 86 a ko wacce gunduma da ke jihar.

Gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal wanda ya sanar da hakan, ya ce manufar kafa cibiyoyin ita ce farfado da al'adar karance-karance tsakanin al'ummarta.

Jihar dai ta yi fice a fagen ilmin addinin Islama, amma kuma ana sanya ta cikin wadanda ke sahun baya a fagen ilmin boko.

A cikin shekara biyu da suka gabata ne gwamnatin jihar Sakkwaton ta kafa dokar ta baci a banagren ilimin jihar.

Hukumomin jihar sun ce cikin abubuwan da aka gano a kan yadda za a bunkasa ilimi a jihar shi ne, a kara yawan cibiyoyin karatu a jihar ta Sakkwato.