Sarkin Katagum, Kabir Umar ya rasu

Sarkin Katagum Kabir Umar ya rasu bayan ya yi fama da jinya
Image caption Sarkin Katagum Kabir Umar ya rasu bayan ya yi fama da jinya

Sarkin Katagum Kabir Umar ya rasu bayan ya sha fama da jinya.

Ya rasu ne a garin Azare jihar Bauchi. Gobe Lahadi ne za a yi jana'izarsa a garin Zaki cibiyar masarautar Katagum.

Daga cikin 'ya'yan da ya bari akwai Baba Kabir Umar, wanda ya taba rike babban sakatare a ma'aikatun gwamnatin tarayya da dama.

Wanda kuma yanzu shi ne hakimin Shira da ke gundumar Katagum.

Shugaban Majalisar Wakilan Najeriya Yakubu Dogara ya bayyana rasuwar sarkin da cewa babban rashin ne ba ga iyalansa kadai ba.

Inda ya ce, "yana mika ta'aziyyarsa ga iyalansa, da masarautar Katagum da jihar Bauchi baki daya."

Sarkin ya mutu yana da shekara 89.

Labarai masu alaka