Matan da suka saka wando a Sudan basu aikata laifi ba

Matan da suka shigar bata dace ba a Sudan na cikin hadarin fadawa hannun 'yan sanda Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Matan da suka shigar bata dace ba a Sudan na cikin hadarin fadawa hannun 'yan sanda

An janye tuhumar da ake yi wa wasu mata 24 wadanda aka kama saboda sun saka wando a wani taron liyafa da aka yi kusa da Khartoum babban birnin kasar.

'Yan sanda sun cafke su ne bayan wani sameme da suka kai yayin taron liyafar a ranar Laraba.

Matan da ake tuhuma za su iya fuskantar hukuncin bulala 40 da kuma tara saboda sun yi shigar da bata dace ba.

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun ce dubban mata ne ake wa bulala duk shekara a kasar bayan an same su da laifin rashin kamun kai.

Har ila yau sun ce dokar hana mata sanya wando da kuma guntun siket tana shafar Kiristocin kasar wadanda su ne tsiraru.

Galibin al'ummar Sudan Musulmi ne kuma mata a kasar suna sanya dogayen tufafi ne bisa al'ada.