Cutar murar aladu ta hallaka dalibai a Ghana

Wannan ba shi ne karon farko da mutane za su fara kamuwa da cutar murar aladu ba Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wannan ba shi ne karon farko da mutane za su fara kamuwa da cutar murar aladu ba

Hukumomin lafiya a Ghana sun tabbatar da cewar cutar murar aladu itace ta yi sanadiyyar mutuwar wasu dalibai hudu a babbar makarantar sakandire ta Kumasi Academy.

Sun kuma ce ana jinyar wasu daliban a wasu asibitoci da ke Kumasi.

A gwaje -gwajen farko da aka yi, an kasa gano cewa cutar ce tayi sanadiyyar mutuwar daliban amma daga bisani an tabbatar da bullar cutar.

Wakilin BBC da kai ziyara yankin ya ce dalibai kalilan ne suka rage a makarantar saboda iyaye sun kwashe 'yayansu daga makaratar.

An kuma dage taron iyayen yara da aka aka shirya yi a ranar Asabar zuwa ranar Litinin.

Sai dai kawo yanzu dai hukumomi na cigaba da bayar da rigakafi ga daliabai da sauran ma`aikatan makarantar.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasu suna cin naman alade a Afirka ta yamma da ma wasu sassan duniya

Labarai masu alaka