Nigeria: An nada sabon Sarkin Katagum

Alhaji Baba Umar Faruk Hakkin mallakar hoto TWITTER
Image caption Ya taba rike babban sakatare a ma'aikatun gwamnatin tarayya da dama

Gwamnatin jihar Bauchi da ke Najeriya ta nada Alhaji Baba Umar Faruk a matsayin sabon Sarkin Katagum.

Sabon sarkin shi ne babban dan marigayi Sarkin Katagum Kabir Umar, wanda ya rasu a makon jiya bayan ya sha fama da jinya.

Lifindin Katagum, Alhaji Magaji Abdulkadir Dahuwa ya shaida wa BBC cewa mutum biyar ne suka nemi sarautar ta Katagum, amma gwamnatin jihar ta zabi Alhaji Baba Umar Faruk.

An haifi sabon Sarkin ne a shekarar 1957 a garin Azare.

Yana da digiri na farko a fannin Tarihi, sannan ya kammala digiri na biyu a fannin Kasuwanci.

Ya taba rike babban sakatare a ma'aikatun gwamnatin tarayya da dama kuma kafin nadin nasa shi ne Hakimin Shira da ke gundumar Katagum.

Image caption Sarkin Katagum Kabir Umar ya rasu a makon jiya

Labarai masu alaka