ECOWAS za ta sa wa 'yan siyasa takunkumi a Guinea

ECOWAS ta yi kira ga masu shiga tsakani da su ci gaba da tattaunawa Hakkin mallakar hoto ERICK-CHRISTIAN AHOUNOU
Image caption ECOWAS ta yi kira ga masu shiga tsakani da su ci gaba da tattaunawa

Kungiyar ECOWAS ko CEDEAO, ta yi barazanar sanyawa 'yan siyasa a kasar Guinea-Bissau takunkumi matukar suka kasa warware rikicin siyasar kasar nan da wata biyu.

Kasar Guinea-Bissau dai ta fada dambarwar siyasa tun lokacin da shugaba Jose Mario Vaz ya kori Firai Minista Domingos Simoes Pereira daga kan mukamin sa.

Fiye da shekaru biyu kenan da tattaunawar sulhu da shugabannin kungiyar ke jagoranta don samar da gwamnatin hadin kai ta ci tura.

Sai dai shugabannin kungiyar a taron da suka kammala a Abuja babban birnin Nigeria, sun yi kira ga masu shiga tsakani da su ci gaba da tattaunawa, koda ya ke kungiyar ta yi takaicin rashin samun wani ci gaba a tattaunawar.

Da ya ke jawabi a taron, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi takaici yadda a koda yaushe kasashen yammacin Afirka ke fuskantar kalubale da dama.

A cewar sa, kalubalen sun hada da tsaro da fataucin bil-Adama inda ya bayyana takaici akan cinikin 'yan ci-rani a matsayin bayi da ake yi a Libya.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaba Buhari ya bayyana takaici akan cinikin 'yan ci-rani a matsayin bayi da ake yi a Libya.

Taron na ECOWAS dai ya kuma duba matsalolin tsaro a yankin kamar rikicin Boko Haram da ayyukan masu tayar da kayar baya a kasashen Mali da Burkina Faso da sauran su.

Wakili na musamman na Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya a yammacin Afirka, Muhammad Ibn Chambers, ya bayyana cewa kafa runduna ta musamman ta kasashen yankin Sahel da aka yi domin yakar masu tayar da kayar baya za ta iya taimaka wa wajen magance matsalar tsaro a yankin.

Labarai masu alaka