Ana tuhumar Puncheon na Crystal Palace da fada da makami

Jason Puncheon na Crystal Palace Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ranar Lahadi da tsakar dare aka kama Jason Puncheon

An tuhumi dan wasan Crystal Palace Jason Puncheon da daukar makami bayan wani fada da suka yi a kusa da gidan rawa a gundumar Surrey da ke kudu maso gabashin Ingila.

An kama Jason Puncheon wanda dan wasan tsakiya ne bayan fadan, wanda suka yi a kusa da mashayar barasa ta Mishiko da ke kan titin Church Street, a Reigate.

An kama dan wasan ne mai shekara 31 a ranar Lahadi da tsakar dare.

Daga bisani aka tuhume shi da mallakar makamin da bai dace ya rike ba, da fada tare kuma da laifin tayar da hatsaniya.

Daga baya aka bayar da belinsa, amma zai gurfana a kotun majistare ta Guildford a ranar biyar ga watan Janairu.

Crystal Palace ta ki ta ce komai game da lamarin.