An haifi jaririyar da aka adana cikinta a kankara shekara 25

Jaririya Baby Emma Hakkin mallakar hoto NATIONAL EMBRYO DONATION CENTER
Image caption An samu cikin jaririya Emma shekara daya da rabi bayan haihuwar babarta

An haifi jaririyar da aka adana cikinta a kankara kusan shekara 25, wanda ya kasance lokaci mafi tsawo tsakanin daukar ciki da haihuwa tun da aka kirkiro da fasahar adana ciki.

Wasu ma'aurata ne da ke Amurka suka bayar da cikin tun a wancan lokacin, wanda hakan ya sa jaririyar ta kasance 'yar matar da ita kanta tana da shekara daya a duniya aka dauki cikin jaririyar.

Cikin da aka bayar wanda ya kasance jaririya Emma Wren Gibson, wadda aka haifa lafiya kalau, an fito da shi ne daga cikin kankarar da aka adana shi a watan Maris, sannan aka dasa shi a mahaifar matar da a yanzu ta haife, mai suna Tina Gibson.

A watan Nuwamban nan aka haifi jaririya Emma.

Madam Gibson wadda take gabashin Tennessee a Amurka, wadda a yanzu take da shekara 26 ta sheda wa CNN cewa, da ba a adana cikin ba tun a lokacin da aka same shi, aka haife shi to da ita da jarirai da aka samu a cikin da kila sun taso a matsayin kawaye.

Ta ce ida dai kawai tana son jaririya ne. Ta ce ba ta damu ba ko wata bajinta ce yin hakan a duniya ko ba bajinta ba ce.

Kungiyar da ta bayar da cikin aka dasa wa matar ta haife shi, tana karfafa wa ma'aurata wadanda ba sa bukatar karin 'ya'ya da su rika bayar da cikin idan sun samu, domin a dasa wa wasu ma'auratan da ba su da 'ya'ya domin su samu haihuwa.