An gano ana 'fataucin' kananan 'yan mata daga Nigeria

Trafficking in Nigerian girls

Mahukunta a Najeriya sun bayyana damuwarsu dangane da wani sabon salon fataucin 'yan mata wadanda shekarunsu basu wuce 15 ba da ake yi zuwa kasashen larabawa.

Wannan ya biyi bayan batun garkuwa da mutane da ya bayyana inda aka gano ana sayar da daruruwan 'yan Najeriya a matsayin bayi a Libya.

Wata jami'a a ofishin shugaban kasa a Abuja ta ce an gano cewa wasu likitoci ne da wasu ejan masu samar wa matafiya izinin shiga kasashen waje ne ke aikata wannan kazamin laifin.

Ba a san dalilan da yasa ake fita da wadannan 'yan matan ba.

Mrs Abike Dabiri ita ce mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan batutuwan da suka shafi 'yan kasar dake zaune a kasashen ketare, ta ce akan samar wa wadannan 'yan matan da shekarunsu suka kama daga 13 zuwa 15 takardun izinin shiga kasashen larabawan na ainihi domin a shigar da su kasashen Saudiyya da Maroko da Masar.

Jami'ar ta yi kira ga hukumar hana fasa kwaurin mutane da ma'aikatar harkokin kasashen wajen Najeriya da su dauki kwakkwaran mataki tun kafin abin ya zama abin da ba za a iya shawo kansa ba.

A makwanni biyun da suka gabata ne aka fara kwashe 'yan Najeriya kimanin 6,000 da suka makale a Libya.

Labarai masu alaka