Wenger da Ferguson: Wa ya fi samun nasara a Premier?

Wenger ya kamo Ferguson Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wenger ya jagoranci Arsenal wasanni 810 a premier.

Arsene Wenger ya jagoranci Arsenal wasannin Premier 810 inda ya yanzu ya yi kafada da Sir Alex Ferguson tsohon kocin Manchester United.

Wenger ya kamo Ferguson ne a wasan da Arsneal ta samu sa'ar Crystal Palace 3-2 a Selhurst Park.

Arsene Wenger zai sha gaban Ferguson a matsayin kocin da ya fi jagorantar wasannin premier a wasan da Arsenal za ta fafata da West Brom a jajibirin farkon shekara.

Arsene Wenger mai shekaru 68, tun a 1996 ne yake jagorantar Arsenal, shekaru 21 da suka gabata.

Kafin 2004, Arsene Wenger ya lashe kofin premier guda uku, amma tun daga lokacin yake farautar kofin.

Wenger da Ferguson.

Duk da cewa Wenger ya kamo Ferguson da yawan jagorantar wasannin premier 810, amma akwai rata tsakaninsu ta fuskar nasorori.

Tazarar nasarar wasanni 60 ne Alex Ferguson ya ba Arsene Wenger.

Arsene Wenger ya lashe wasanni 467, Ferguson kuma ya samu nasara a wasanni 528.

Wenger ya sha kashi a wasanni 145, yayin da Ferguson ya sha kashi a wasanni 114.

An ci Wenger kwallaye 779 a Arsenal, Ferguson kuma 703.

Sannan Farguson ya fi cin kwallaye inda ya ci 1,627, Wenger kuma 1,521

Kofi 13 na lig Fergusaon ya lashe inda ya ba Wenger tazarar kofi 10, yayin shi kuma ya ci guda uku.

Labarai masu alaka