Cairo: Dan bindiga ya kai wa Kiristoci Kibdawa hari a coci

Wani mutum na duba ramukan harbi a jikin cocin Mar Mina bayan harin da aka kai a gundumar Helwan na birnin Alka'ira. Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wani mutum na duba ramukan harbi a jikin cocin Mar Mina bayan harin da aka kai a gundumar Helwan na birnin Alka'ira.

Hukumomi a Masar sun ce mutum tara sun rasa rayukansu bayan da wani dan bindiga ya kai hari a wani coci da wani shago mallakin mabiya kirista a Helwan da ke kudancin Alkahira babban birnin kasar.

Rahotannin farko na cewa jami'an tsaro sun kashe dan bindigan, amma ma'aikatar cikin gida ta ce yana hannu kuma rauni kawai ya samu.

Wannan harin ya zo ne dab da bukukuwan sabuwar shekara da kuma bikin kirsimetin kibdawa da za a yi ranar 7 ga watan Janairu.

A shekarar da ta gabata, an kashe fiye da kirista dari a hare-haren bam da na 'yan bindiga a Masar, kuma reshen kungiyar IS a kasar ne suka dauki alhakin kai hare-haren.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jami'an tsaro na sintiri a sassan babban birnin Alkahiira

Labarai masu alaka