Tanzania za ta rufe coci-coci ma su sukar Magafuli

John Magafuli Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption John Magufuliya musanta cewa yana mulkin kama-karya ne, duk da yadda yake dira kan masu sukar salon mulkinsa

Hukumoni a Tanzania sun yi gargadin cewa za su rufe dukkanin mujami'un kiristocin kasar da ke gauraya addini da siyasa, bayan da wani malamin addini ya soki shugaba John Magufuli a wani wa'azi na bikin kirsimeti.

Malamin addinin, Zachary Kakobe ya ce kasar na kan hanyar komawa wacce ake mulki a karkashin jam'iyya daya tilo.

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta ce za a soke lasisin duk kungiyar addinin da ta yi sharhi na siyasa game da salon mulkin shugaban kasar.

Masu sukar gwamnatin kasar na cewa lamarinta ya fara wuce gona da iri, inda a baya ta rufe jaridu kuma ta hukunta mutane da dama kan abin da gwamnatin ta kira sun ci zarafin shugaban kasar a shafukan sada zumunta na intanet.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana kiran Magafuli "bulldozer" saboda salon mulkinsa

Tsarin mulkin Tanzaniya ya tabbatar wa kowa 'yancin addini, duk da cewa ana bukatar kungiyoyin addinin su yi rajista a ma'aikatar cikin gida kafin su fara gudanar da ayyukansu.