MDD ta taya sabon shugaban Liberia Murna

George Weah
Image caption Tun a shekarar 2005 ne Mista Weah ya fara tsayawa takarar shugaban kasar Liberia

Babban magatakardar MDD ya mika sakon taya murna ga sabon shugaban Liberia kuma tsohon fitaccen dan wasan kwallo George Weah kan nasarar da ya yi a zaben da aka gudanar a kasar.

Antonio Guterres ya kuma yabawa mataimakin shugaban kasa, kuma abokin takarar mista Weah wato Joseph Boakai da ya amince da shan kaye ba tare da wata hatsaniya ba.

Ya kara da cewa zaben da aka gudanar bisa gaskiya ta adalci 'yar manuniya ce da ke nuna zaman lafiya da kwanciyar hankali ya samu zama a kasar.

Sai dai yace akwai kalubale da aiki Ja ga sabon shugaban na ciyar da Liberia gaba, dan haka ya ce hada kai tsakanin 'yan kasar da 'yan siyasa abu ne mai matukar muhimmanci dan ciyar da ita gaba.

Jim kadan bayan samun labarin nasarar ta Mista Weah, magoya bayansa suka fara bukukuwan nuna murnarsu a babban birnin kasar na Monrovia.

Yakin neman zaben Mista Weah a karkashin hadakar jam'iyyun siyasa ta CDC - Coalition for Democratic Change - ya burge matasa sosai, amma abokin takararsa kuma mataimakin shugaban kasa Mista Boakai bai sami karbuwa sosai ba.

Kuma matar tsohon shugaba Charles Taylor, Jewel Taylor ce mataimakiyarsa, duk da cewa shi Charles Taylor din na tsare a wani gidan yari dake Burtaniya a sanadiyyar samunsa da laifukan yaki da aka yi a makwabciyar kasar Saliyo.

A watan Oktoba, Mista Weah ya lashe zagayen farko na zaben shugaban kasa da aka gudanar, inda ya sami kashi 38.4 cikin dari, shi kuwa mai binsa a baya, Mista Boakai dan shekara 73 ya samu kashi 28.8 cikin dari.

Rashin samun wanda yayi nasara kai tsaye ne ya janyo aka gudanar da zaben a zagaye na biyu.

Hukumar zaben kasar ta Laberiya ta ce an kammala kidayar kashi 98.1 cikin dari na kuri'un da aka kada, kuma zuwa ranar yau Alhamis, Mista Weah ya lashe kashi 65.5 cikin dari na kuri'un.

Mista Boakai kuma na da kashi 38.5 cikin dari ne na dukkan kuri'un.

Labarai masu alaka