Abin da na fada wa Buhari - Abdulmumini Jibrin

Abdulmumini Jibrin da Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto A. Jibrin
Image caption Dan majalisar wakilai Abdulmumini Jibrin tare da shugaba Muhammadu Buhari a lokacin ganawarsu.

Wani dan majalisar wakilai da aka dakatar saboda badakalar cushe a kasafin kudin kasar na shekara ta 2016 ya gana da Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Abdulmumini Jibrin shi ne dan majaisa mai wakiltar mazabar Kiru/Bebeji ta jihar Kano.

Jibrin ya gurfanar da shugabannin majalisar a gaban wata kotu bisa zargin dakatar da shi ba bisa ka'ida ba.

Ya shaida wa BBC cewa ganawar ta sa da Shugaba Buhari za ta zama sanadin warware matsalar da ta kai ga dakatar da shi daga majalisar.

Ya ce sun tattauna game da "Abubuwan da suka shafi harkokin siyasar kasa da kuma abubuwan da suka shafi dakatar da ni da mazabata a majalisa."

Da aka tambaye abin da ya fada wa shugaba Buhari game da batun dakatar da shi da aka yi daga zaman majalisar wakilan, sai ya ce:

"Ka ga irin wannan zaman, daga ni sai shi, sai kuma Allah... Amma ina tabbatar maka da cewa zama ne aka yi mai kyau, kuma an sami kyakkyawar nasara kuma na fito cikin farin ciki".

Majalisar wakilai ta ce ta dakatar da dan majalisar ne saboda ya fallasa lamarin cushen kasafin kudin Najeriya.

Batun cushe a kasafin kudin ya tayar da kura, ko da yake shugabannin majalisar karkashin jagorancin Yakubu Dogara sun sha musun aikata ba daidai ba.

Amma dan majalisa Jibrin ya dage da cewa dakatawar da aka yi masa ba bisa ka'ida take ba.

"Yau wata 16 muna kotu, duk da muna ganin girman kotu, amma abin in ka kalle shi ta wata fuska abin mamaki ne."

Ya kara da cewa "Karar da muka shigar a kotu abu ne da ba ya daukar lokaci fiye da wata uku kotun ta yanke hukunci. To amma kararmu ta yi wajen wata 15 a kotu."

Ya ce karar da ya shigar ta nemi kotu ta fayyace ko "Majalisar kasa tana da ikon ta dakatar da dan majalisa?"

Ya kuma nuna rashin gamsuwarsa da yadda majalisar wakilan ta dakatar da shi har na tsawon kwana 180 a karon farko.

"Kwana 180 din sun zo sun wuce, amma an ki a mayar da ni gidan. An ce kuma sai na bada hakuri."

Da aka nemi ko ya bayar da hakurin, sai ya ce:

"Ba abin da gwamnatin Kano ba ta yi ba da Dogara, kuma ta bada hakuri. Sarkin Kano ya sa baki. Majalisar jihar Kano a dunkule sun bada hakuri."

Ya tuhumi shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara da kin mayar da shi bayan da ya bukaci dukkan 'yan majalisar jihar ta Kano da shi kansa Abdulmumini Jibrin su rubuta takardar bada hakuri.

Ya ce sun cika dukkan sharuddan da Yakubu Dogaran ya nemi a cika domin warware matsalar, amma har yanzu bata sauya zani ba.

"Kaga wannan sai ya nuna cewa ba hakuri yake nema ba, akwai wani abin da ake nema."

BBC ta yi kokarin jin ta bakin shugabancin majalisar wakilan Najeriya kan wannan batu, amma hakarmu ba ta cimma ruwa ba.

Labarai masu alaka